Kiran wanin Allah

Tawassuli baya nufin cewa wanda ake tawssuli dashi yana da kudira da iko koma bayan Allah ba a kan biyawa mutum bukatunsa, kuma yana nufin ana bauta masa bani, sai dai ana tawassuli da shi ne saboda Allah ya yi umarni da haka.

Allah (t) ya tsara wannan rayuwa ta duniya a kan abin da ake ce masa sabubbba, kamar yadda Allah (T) yake cewa: "mun sayna sababi ga kowane abu", duk wani abu da ka gani a wannan duniya to yana da dalili, babu banbanci ata bangaren addini ko kuma ta bangare rayuwar yau da kullum ne, misali idan mutum bas hi da lafiya zai sha magani sai ya sami lafiya domin haka Allah ya tsara, don haka idan mutum yana da wata bukata a wajan Allah akwai wadanda Allah ya sanya su suka fi kowa kusanci dashi sai ya yi kamun kafa da su.

AttachmentSize
File 12796-f-hoosa.mp431.47 MB