ABDULLAHI DAN SABA'A 2

Tatsuniyar Abdullahi dan saba'a ta zamanto wani makami da makiya makarantar Ahlul Baiti (as) suke amfani da shi don ganin sun kafirta mabiya wannan makaranta, duk da cewa ita wannan Magana ba ta da wani tushe ballantana makama. Abinda wannan tastuniyar t

 Tatsuniyar Abdullahi dan saba'a ta zamanto wani makami da makiya makarantar Ahlul Baiti (as) suke amfani da shi don ganin sun kafirta mabiya wannan makaranta, duk da cewa ita wannan Magana ba ta da wani tushe ballantana makama.

Abinda wannan tastuniyar take cewa shi ne wai wani Bayahude ne ya kafa akidar Shi'a a lokacin Usmanu dan Affan.

Wannan tastuniya an samota daga wani mutum wanda ake ce masa Saifu dan Umar, duk wanda ya rawaici wannan Magana ko a kowane littafi ne to daga wannan mutumin aka samota.

Malaman Hadisi sun tabbatar da cewa: wannan mutum wato Saifu dan Umar makaryace ne, yana kirkirar hadisai yana danganasu da Annabi (saww) alhali ya san karya yake, sannan kuma shi dai Saifu dinnan fasiki ne, zindiki ne.

Annabi (saww) shi ne ya sanyawa mabiya Imam Ali sunan Shi'a.

AttachmentSize
File ABDULLAHI DAN SABA'A 235.64 MB

Ƙara sabon ra'ayi