Kadaita Siffofin Allah

Allah shi kadai ne a siffofinsa, kuma siffofinsa su ne ainihin zatinsa, yawan siffofi a ma’ana ba yana nufin yawan zatinsa a samuwarsa ba, sai dai zatinsa daya ne, siffofinsa duk suna bayanin wannan zatin ne. Ya zama wajibi a kadaita Allah a siffofinsa domin siffofinsa ainihin zatinsa ne. Kamar yadda kore siffofin kamala ga Allah bai dace ba domin wannan yana kaiwa ga cire masa dukkan wata kamala. Allah ya tsarkaka daga rashin kamala.

AttachmentSize
File 8a0d43385efe2f70812b5d4a968fde04.mp414.41 MB

Ƙara sabon ra'ayi