Bidi'a a Cikin Addini

Salafanci ko Wahabiyanci da aka fi sani da sunaye daban-daban kamar izalatul bidi'a a nigeria ko salafawa, ko albanawa a yau da sauran sunaye daban-daban. Wahabiyanci ya fara daga Ibn Taimiyya a karni na bakwai hijira sannan sai ya samu kafa masa daula a hannun Muhammad bn Abdulwahab a saudiyya karkashin taimakon ingila. Wannan fikirar ta taso ne daga kokarin fassara ma'anar shirka da kafirci ta yadda Ibn Taimiyya ya kawo fahimtarsa wacce duk malaman musulmi suka saba masa a kanta da sabani mai yawa, sai dai an zakulo ta domin cimma hadafin da 'yan mulkin mallaka suka ga zai zama mai amfani wurinsu don tarwatsa kan musulmi.

AttachmentSize
File 3c5f8f6c2011aa4b023fb31b9695ec18.mp413.66 MB

Ƙara sabon ra'ayi