TARIHIN IMAM HUSAIN( AS) (13)

 
Sai ya ce: ya muhammad! Na yi duba izuwa ƙasa, sai na zaɓeka daga cikin ahalin ƙasa, sai na tsaga maka suna daga cikin sunayena, ba za’a ambaceni ba a wani waje face sai an ambaceka tare dani, ni ne Mahmud, kai ne Muhammad.
Sai na ƙari yin duba na biyu  izuwa kasa, sai na zaɓi Alyyu, na na tsaga masa suna daga sunayena, ni ne Ala’ala shi ne shi ne Aliyyu.
Ya Muhammad! Haƙiƙa ni na halicceka kuma na halicci Aliyyu da Faɗima, da Faɗima da Hasan, da Husaini, ƴ’aƴ’ansu, daga nau’in wani haske daga haskena, sannan na bijiro da wilayarsu, ga ahalin sammami da ƙassai, wanda ya karɓeta shi ne zai kasance daga miminai a wajena, wanda kuma ya yi jayayya da ita a wajena zai kasance daga cikin kafirai.

Ƙara sabon ra'ayi