ANNABTA (3)

Da a ce: Allah bai aiko ƴ’an saƙon da za su nunawa mutane yadda za su bauta masa ba, kuma da annabawa basu nuna mutane yadda za su kusance shi ba ta yadda za su sami kamala ta har abada ba, da hakan ya sanya munufar da Allah ya halicci mutane saboda ita ta rushe.
Wannan shi ne ake ce masa (نقض الغرض) warwarar munufa, wannan kuwa duk mai hankali baya aikata irin wannan aiki, kamar a ce: yau ga wani mutum ba shi da gida, sai ya gina gida saboda shi da iyalansa su zauna, amma sai ya ƙi gina kofar da za a shiga gidan, bayan ya gama ginin gidan, sai ya ƙi shuga ciki kuma ya ƙi shigar da iyalansa don su zauna a ciki, sai su zauna a waje ruwa yana ta dukan su,  to a nan za muga cewa duk mai hankali da hikima ba zai aikata haka ba, ballantana Allah wanda bashi da buƙata, shi ne cikakken mawadaci, ya halicci mutum da aljan don su bauta masa to ashe wajibi ne ya nuna musu yadda za su bauta masa har su sami kamalar ta har abada wacce ya halice su don ya basu.

AttachmentSize
File c53ef112cbd649fae73089b575102ba5.mp418.98 MB