TARIHIN IMAM HUSAIN( AS) 18

Isar imam Husain zuwa Karbala

Da hantsin ranar biyu ga watan muharram shekara ta sittin da ɗaya bayan hijira imam Husaini da tawagarsa suka isa Karbalaa,  a wannan rana ce ya faɗi wannan shararriyar maganar tasa wacce yake cewa:

Nan ne wajan  baƙin ciki da bala’i, nan ne wajan tsayawar tawagarmu, shi ne zangon tafiyarmu, shi ne wajan kashe mazajenmu, shi ne wajan wajan zubar da jinanenmu.

A cikin wannan rane Umar ibn Sa’ad Allah ya tsine masa albarka ya isa Karbala, a tare da shi akwai mayaƙa dubu huɗu.
A cikin rana 5 ga watan Muharram ne adadin mayaƙan Yazudu tsinanne ya kammala, suka yi sansani don yakar imam Husaini (as) da iyalnsa da, kuma shabbansa, Allah ya ƙara yarda a garesu gabaɗaya

A rana ta biyar ne annabi Musa (as) da jama’rs suka tsallake kogi, sannan Fir’auna da jama’arsa suka halaka.
 

AttachmentSize
File c1a1d27696c22671ac430410f6af1c68.mp425.79 MB

Ƙara sabon ra'ayi