IMAMANCI (3)

A makarantar Ahlul Baiti (as) imama tana daga cikin Usuluddin, don haka mutum ba zai kasance mabiyin makarantar Ahlul Baiti ba face sai ya yi imani da cewa Manzon Allah (saww) ya bar mana khalifofi guda goma sha biyu na farko shi ne imam Aliyyu (as) sai imam Hasan bayansa sai imam Husaini na ƙarshensu kuma shi ne Imam Mahdi Allah ya gaggauta bayyanarsa.
Ammam a makarantar Ahlussuna sun tafi a kan cewa imama ba ta daga cikin usuluddini, tana daga cikin furu’uddini, wato matsayinsu ɗaya da salla, azumi sa zakka, da sauransu.
Sannan makarantar Ahulul Baiti sun tafi a kan cewa Allah shi ne yake da ikon ya naɗa khalifan Annabi (saww), mutane ba su da alhakin su zaɓi khalifa.
Ammam makarantar Ahlussuna sun tafi a kan cewa mutane su ne suke da haƙkin su zaɓi khalifa. 

AttachmentSize
File a36d7bc73106d984c907b7aa6fd5e4ef.mp416.36 MB

Ƙara sabon ra'ayi