An Bukaci Da A Gudanar Da Bincike Kan Kisan Gillar Da Aka Yi A DR Congo

Gamayyar kungiyoyi fararen hula a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta bukaci gudanar da bincike kan kisan gillar da aka yi wasu fararen hula a wani kauye da ke gabashin kasar.

 

 

A sanarwar da gamayyar kungiyoyin fararen hula ta Club Nyirangongo a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta fitar a jiya Lahadi ta jaddada bukatar hanzarta gudanar da bincike kan kisan gillar da aka yi wa wasu fararen hula biyar a cikin daren Asabar wayewar garin Lahadi a kauyen Nyanzale da ke yankin Rusthuru a lardin Kivu ta Arewa.

 

Wasu rahotonni suna bayyana cewa; Rikici ne ya kunno kai tsakanin 'yan gudun hijira da al'ummar kauyen na Nyanzale lamarin da ya janyo hasarar rayuka.

 

Babban sakataren gamayyar kungiyoyin ta Club Nyirangongo a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo Innocent Segihobe ya jaddada cewa; Dole ne mahukuntan kasar su hanzarta gudanar da bincike kan matsalar domin magance sake bullar makamancin haka a nan gaba.

Ƙara sabon ra'ayi