Iran Ta Gargadi Saudiyya AKan Tura Dakaru Siriya

Iran ta kuma bukaci Riyad data dakatar da hare-haren da take jagoranta a kasar Yemen.
Ministan warkokin wajen kasar Iran Mohammad Zarif, ya yi kashedi ga Saudiyya akan batun tura dakarun ta a kasar Siriya.
Mr Zarif wanda ke bayana hakan jiyya a yayin wani taro manema labarai a zauren majalisar Turai a Bruxells, ya kuma bukaci Riyad data dakatar da hare-haren da take jagoranta a kasar Yemen.
Kazalika Mr Zarif ya kara da cewa duk wadanda suka shiga Siriya ba tare da izinin gwamnatin kasar ba, na keta dokokin kasa da kasa ne.
Mr Zarif dai na masa tambayoyin manema labarai ne akan ikirarin Saudiyya na cewa tana nazarin tura dakarun ta na kasa a Siriya domin yaki da 'yan ta'ada, wanda a cewar Mr Zarif tura dakaru barkatai zai kara dagula al'amura a Siriya wanda kuma zai iya zama babban hadari a yankin gabas ta Tsakiya.
Da yake amsa tambaya manema labarai akan cewa Iran nada sojoji a Siriya, Mr Zarif ya ce Iran ba tada Sojoji a Siriya aman tana da mashawartan sojojin ta wanda ta aike bisa bukatar gwamnatin Syria.

Ƙara sabon ra'ayi