Taron Amurka Da Kawayenta Kan Syria

Taron Amurka Da Kawayenta Kan Syria Taron Amurka Da Kawayenta Da 'Yan Koranta Kan Syria A Birnin Rom Na Kasar Italiya

Taron Amurka Da Kawayenta Kan Syria
Taron Amurka Da Kawayenta Da 'Yan Koranta Kan Syria A Birnin Rom Na Kasar Italiya
A jiya ne aka gudanar da taron Amurka da kawayenta da ke daukar nauyin rikicin kasar kasar, taron da aka fi sani da abokan Syria a birnin Rom na kasar Italiya, wanda ya hada ita kanta Amurka, da kuma wasu daga cikin kawayenta turawa, sai kuma wasu 'yan koranta dag cikin kasashen larabawa gami da Turkiya.   Taron dai ya mayar da hankali ne kaco kaf kan irin taimakon da zai bayar wajen kara azuzuta wutar rikicin Syria, maimakon hanyoyin da za a bi wajen samun sulhu da kawo karshen rikicin ta hanyar tattaunawa tsakanin bangarorin rikicin, inda dukkanin mahalarta taron suka mayar da hankali kan batun kara yawan makaman da suke tura ma 'yan bindiga a kasar Syria domin aiwatar da abin da Amurka ta ce tana bukata tun farkon rikicin na Syria, wato kawo karshen gwamnatin shugaba Bashar Assad wanda baya dasawa da ita kuma yake a matsayin barazana ga Isra'ila.   A lokacin da yake gabatar da jawabinsa a gaban taron, sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya jaddada wajabcin taimakon 'yan bindiga a kasar Syria, domin abin da ya kira gaggauta kawar da gwamnatin shugaba Assad, kamar yadda ya bayyana cewa Amurka za ta bayar da karin taimako ga 'yan bindigar na kasar Syria da zai kai na dala miliyan 60, tare da ba horan soja.   A makon farko na watan Fabrairun da ya gabata ne dai jaridar The Sunday Times da ake bugawa a kasar Birtaniya ta bayar da wani rahoto da ke cewa, tun a karshen shekarar da ta gabata ne gwamnatin Amurka ta fara bayar da makamai kai tsaye ga 'yan bindiga na kasar Syria, baya ga wadanda take bayarwa ta hanyar gwamnatcin Saudiyya, Qatar da kuma Turkiya, da suka hada manyan bindigogi, makaman roka, da makaman harbor jirage da a wasu makaman da ba asani ba, daga cikin wadanda suke samun wadannan makamai kuwa har da kungiyar Jabhat Nusra, reshen kungiyar alkaida a kasashen Jordan, Syria, Palastine da kuma Lebanon, wadda ita ce kan gaba wajen jagorantar ayyukan ta'addanci a halin yanzu a kasar Syria da sunan yunkurin kawar da shugaba Assad, inda kungiyar take daukar nauyin hare-haren bama-bamai da da kunar bakin wake da ake kaiwa a sassa daban-daban na kasar Syria, wanda hakan kan yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da dama, na baya-bayan nan shi ne wanda kungiyar ta kai a birnin Damascus, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula fiye da 90, da suka hada da mata da kuma kananan yara 'yan makaranta.   Ita kuwa jaridar The New York Times a bugunta na ranar Lahadi da ta gabata, ta bayar da wani rahoto ne dangane da cinikan makamai da aka yi tsakanin gwamnatin Saudiyya da kuma gwamnatin kasar Crotia tun a cikin watan Disamban 2012, inda kuma yanzu haka wani adadi mai yawa na wadannan makaman ya isa ga hannun 'yan bindiga na kasar Syria ta hanyar gwamnatin Jordan, jaridar ta ce ta tuntubi mahukuntan Crotia kan wannan batu, amma sun ce ba su masaniya kan cewa wadannan makamai za a kai su 'yan bindiga na kasar Syria ne, amma a lokacin da jaridar ta tuntubi mahukuntan Saudiyya da Jordan, sun ki su ce uffan kan wannan batu.   Da dama daga cikin masana harkokin siyasar yankin gabas ta tsakiya, sun yi ammanar cewa wannan mataki na taron Amurka da kawayenta gami da 'yan koranta kan Syria, ya zo ne sakamakon gazawar da 'yan bindiga ke nuna a fili a gaban sojojin Syria, da kuma kisan da ake yi musu a kulum rana ta Allah, wanda hakan ke nuni da cewa idan har lamarin ya ci gaba da tafiya  a hakan, to ko shakka babu dakarun gwamnatin Syria za su murkushe sun an ba da jimawa ba, musamman ganin cewa akasarin wadanda ake kira 'yan tawaye a kasar ta Syria ba su da masaniya kan kan kasar, kasantuwarsu baki ne da suka zo daga kasashe daban-daban domin aiawatar da wannan manufa ta Amurka da kasashen yammacin turai a Syria, kodai a matsayin sojojin haya, ko kuma da sunan jihadi.

Ƙara sabon ra'ayi