YAKIN JAMAL

YAKIN JAMAL

                    Kafin Annabi (saww) ya yi wafati ya yi bayanin abubuwa da yawa da za su afku a tsakanin musulmi kamar sabani harma da yake-yaken da za su yi, kuma ya yi bayanin wadanda suke tare da Allah da Annabinsa kuma su ne wadanda suke tare gaskiya.

Yakin jamal yake ne wanda uwar muminai A'isha ta jagoranta, inda ta yaki Imamu Ali (as) duk da cewa shi ne khalifan Annabi (saww) a wannan lokaci, game da cewa  Annabi ya gargadeta da yin wannan aiki, kuma ya nuna mata cewa idan ta sami kanta wannan hali to ba ta da gaskiya.

 Imam Ali (as) ya yi duk iya yadda zai don ya saki nuna musu cewa bai halatta ba su yakeshi kuma ya yi kokarin ya sake tunatar da su a bin da suka riga suka sani cewa Annabi (saww) ya fada ya nanata cewa: "duk wanda ya yaki Ali (as) babu shakka Annabi ya yaka". amma ba su yarda ba sai da suka afka masa da yaki.

Ƙara sabon ra'ayi