Imam Mahdi

Imam Mahdi

babu sabani  tsakanin muslmi Shi`a da Sunna kan bayyanar Imam Mahdi a karshn zamani, wato lokacin da duniya ta cika da zaluci, zai zo ya tumbuke wannan zaluncin kuma ya kwatowa wadanda aka zalunta da raunana hakkokinsu, da kafa tsantsar adalci a ban kasa, gami da daukar fansar mummunan zaluncin da aka yiwa Annabi(saww) da iyalan gidansa. Wannan batu kuwa hadisai ingantattu  masu yawa sun yi Magana a kansa daga manyan littattafan Sunna da na Shi`a wadanda za mu kawo wasu daga cikinsu a nan gaba.                                                   

 An karbo daga Huzaifah ibnul Yamani ya ce: Manzon Allah (saww) ya yi mana huduba sai mazon Allah ya tunatar da mu abin da ya ke kasantacce, sannan ya ce: da babu abin da ya yi saura a duniya sai yini daya da Allah madaukakin sarki  ya tsawaita wannan yini har sai ya tayar da wani mutum daga `ya`yana a cikinsa, sunansa kamar Sunana. 

Abdullahi dan Umar ya rawaito cewa manzon Allah (saww) ya ce: (a karshen zamani wani mutum daga yayana zai fito sunansa kamar sunana (Muhammad) alkunyarsa kamar alkunyata, zai cika duniya da adalci kamar yadda ta cika da zalunci wannan kuwa shine Mahdi).                    

Abu Na`im  ya rawaito daga Abdullahi dan Umar cewa: Isa Dan Maryam zai sauko duniya, kuma zai yi sallah a bayan Mahdi).                                  

AttachmentSize
File 13106.f.hoosa_.mp435.69 MB