Rayuwar Mace a Al'ummu Magabata - 3

Dan'adam yana bukatar rayuwar tarayya cikin al'umma wacce ba ya iya rayuwa ba tare da ita ba, akwai alakoki masu yawa da suka hada alakokin mutane iri-iri, sai dai mafi karfin alaka ita ce tsakanin miji da mata a zamantakewar auratayya da ke tsakaninsu. Mace ta fuskanci zalunci mai tsanani a tarihin dauloli da suka wuce a shekaru aru-aru, a nan mun kawo misalan wasu daga cikin irin wadannan zaluncin da ta fuskanata da ya hada ribace ta, rashin wani hakki a al'umma, rashin lissafa ta cikin al'umma, da sauransu. Sai dai taken da musulunci ya kunsa kuma ya shelanta wa duniya shi ne; Babu wani tsakanin namiji da mace wanda ya fi wani daraja a wurin Allah sai da takawa.

Ƙara sabon ra'ayi