Kamalar Kur'ani

Littafin Allah mai girma mai daraja Kur'ani saukakke daga gare shi littafi ne da ya kammala babu dadi babu ragi. Allah madaukaki da kansa ne ya ba wa annabinsa umarnin jera komai nasa, don haka jera kalmominsa da ayoyinsa, da jumlolinsa baki daya saukarwa ne daga Allah madaukaki. Sai dai an yi sabani kan cewa waye ya jera surorinsa, mu a nan mun zabi ra'ayi mafi dacewa cewar hatta da surorinsa annabi ne da kansa ya jera su, don haka babu wani wanda yake da hannu wurin tsara komai a Kur'ani, duk abin da ya shafe shi tsarawa ne daga Allah ubangijin talikai.

AttachmentSize
File f95cca28eb4d7b6d7ee74f5a7c2be779.mp49.12 MB

Ƙara sabon ra'ayi