In Taimiyya da tauhidi Ma’anar tahidi

Babu shakka sanin ingantacciyar aƙida ta musulunci shi ne farkon ilimin da ya wajaba ga dukkan musulmi ya fara sani, saboda idan ita akida bata inganta ba to babu wata ibada da za a karɓa daga mutum, mutuƙar aƙida bata inganta ba, to ibada ba za ta taɓa zama ingantacciya ba, ma’anar ilimin akida kuwa kokuma ilimin tauhidi shi ne ilimin da yake bincike a kan mahaliccin halitta, zatinsa siffofinsa, da ayyukansa, sannan dalilin da ya sa muke bicike a kan mahaliccin halitta kuwa shi ne: duk mutum yana da wasu tambayoyi guda uku da ya ke da buƙatar amsarsu, waɗannan tambayoyi kuwa su ne: ta ɗaya shin daga ina yake wato menene mafarinsa? A ina yake? Ta uku bayan wannan rayuwa kuma ina zai koma, sanin amsoshin waɗannan tambayoyi shi ne yake mai da mutum mai addini kokuma mara addini
 

AttachmentSize
File 3c3e3748edeee60137568a60decee47b.mp422.43 MB