TAUHIDIN IBN TAMIYYA YA YA SAƁA DA TAUHIDIN AHLUL BAITI (4)

Imaman Ahlul baiti (as) sun tabbatar mana da cewa kamar yadda Alƙur’ani ya tabbatar mana da cewa Allah yana da siffofi haƙiƙa yana da siffofi, amma haka ba yana nuna cewa zai yiwu wani ya iya san haƙiƙanin zatin Allah ba, amma hakan ba yana nufin cewa kwata – kwata ba bu wanda zai iya sanin Allah ba, abin nufi a nan shi ne cewa akwai gwargwadon sani da ɗan Adam zai iya yi, wannan kuwa shi ne abin da ya zama wajibi ga duk mutum.
Imam Aliyyu (as) yana cewa ( duk waɗanda suka daidaita da Allah da ababan halitta to sun yi ƙarya, kuma sun yi ƙafircewa abin da Allah ya saukar na ayoyi muhkamai, sune waɗanda suka cewa Allah yana da gaɓɓai, suka baiwa Allah siffofin ababan halitta).
 

AttachmentSize
File ddc64692d15204ac467e0eecf9c1b824.mp415.01 MB