ANNABTA (6)

Malaman ilimin kalam sun yi saɓani a cikin sauran rayuwar annabawa cewa idan ba wajan isar da saƙo ba, shin haka nan wajibi ne annabawa su kasance ma’asumai, sannan yau she ne annabi yake kasancewa ma’asumi a cikin rayuwars? a kwai maganganu a kan haka za mu kawo su a taƙaiace, su ne kamar haka:1-     Dole ne annabi ya kasance ma’asumi a wajan tablig da isar da saƙon manzancinsa kawai.2-     Wajibi ne annabi ya kasance ma’asumi wato ya kasance kwata – kwata baya aikta saɓo karami ne kokkuma babba, yana sane ne kokuma bisa kuskure ne, sannan ya kasance ma’asumi a cikin dukkanin  al’amuwansa na yau da kullum, ba wai sai kawai wajan isar da saƙo ba, wannan shi ne ra’ayin makarantar iyalan gidan annabi Muhammad (saww).3-     Wajibi ne annabi ya ksance ma’asumi wato ya ksance baya aikata manyan zunubai, yana sane ne kokuma bisa kuskure, amma a bisa wannan ra’ayi koda ya kasance yana aikata ƙananan zunubai to hakan baya hana shi ya warware ismarsa, wannan shi ne ra’ayin mu’utazilawa. Annabi ma’asumi ne wajan barin aikata manyan zunubai, da kuma ƙanana, amma idan yana sane, wato a bisa wannan ra’ayi da ace annabi zai aikata manyan zunubai, kokuma ƙanana bisa kuskure, to hakan baya rusa ismarsa, wannan shi ne ra’ayin Ash’ariyywa.

AttachmentSize
File a41180c4f2d306e1d4972b4529d502ed.mp421.3 MB

Ƙara sabon ra'ayi