ANNABTA (5) - Abubuwan da ake gane annabawa da su

Abubuwan da ake gane annabawa da su
 
Ana gane annabawa ta abubuwa guda uku
 
1-    Wanda ya yi da’awar annabta kada ya zo da abin da ya saɓawa hankali, kamar ya ce: Allah ba ɗaya bane.
 
2- Wanda ya yi da’awar annabta ya kasance yana kira ne izuwa ga ɗa’a da biyya ga Allah (t), da kuma barin duk abin da ya saɓa masa.
 
3- Wanda ya yi da’awar annabta ya kasance ya zo da mu’ujizar da za ta ƙarfafi annabtarsa, wacce take tare da ƙalubantar duk wanda bai yadda da annabtarsa ba, kuma ta gajiyar da su, ta yadda babu wanda zai iya zuwa da abin da ya zo da shi.
 
Mu’ujiza
 
Mu’ujiza ita ce: aikin da ya keta al’ada, wanda wani mutum banda annabi babu wanada zai iya zuwa da shi.Saboda wannan gazawar it ace ake cewa tahaddi ( ƙalu bale), wato shi bannabin ya cewa al’ummarsa: idan ba ku yadda da cewa ni annabi bane, to idan kun isa ku aikta irin wannan aikin da na aikata.

AttachmentSize
File 68fea7d1a2423f5056be7eb22c5aa06c.mp425.59 MB

Ƙara sabon ra'ayi