Ibna Taimiyya da tauhidi Malaman Ahlussuna sun tafi kana cewa bai halatta a ce Allah Yana sama ba

 
 
 Malaman makarantar Ahlusunna sun tafi a kan cewa da Allah yake cewa: ya daidaita a kan al’arshi, to ba za a fassara shi da cewa Allah yana zaune a kan al’arshi ba, domin a bisa domin haka mustahili ne, ba zai yuwa a ce Allah ya zauna a kan wanigado ba, kokuma a ce ya keɓanta da wani waje, domin haka babu abin da yake nunawa sai kamanta Allah da ababan halitta, alhali a cikin Alƙur’ani mai girma Allah yana cewa ( babu wani abu da ya yi kama dashi.
Daga cikin waɗanann malamai akwai Albaihaƙi, Alkadhi iyadh, Alƙurɗubi, alkhalili, Aɗɗahawi da makamntansu.
Akwai wasu malaman kuma da suka tsaya ba sa kutsawa cikin wadannan ayoyi su fasara su da gundarin ma’anarsu  wacce take nuna naƙasu ga Allah, don haka sai suka tsaya basa fassara su, idan ka ce menene istiwa’i sai su ce Allah shi kaɗai shi ne ya san menene ya ke nufi da shi, daga cikin irin waɗananna malai akwai imam Malik wanda ake dangana mazhabar malikiyya izuwa gareshi.

AttachmentSize
File 5ce6e761fb435f84bcb86ca809d0c62f.mp413.68 MB