Ibn Taimiyya da tauhidi Wanda ya ce Allah yana ko’ina To ya ce komai Allah ne

 
Ib taimiyya yana cewa: Allah yana sama yana zaune a kan al’arhinsa, sannan duk wanda ya ce: Allah yana ko’ina to shi kafiri ne, kai kafircinsa ma ya fi na kafirai , saboda wanda yace ubangijinsa shi ne gunki, to zai kasance wannan gunkin kawai yake bautawa, wanda kuwa ya ce Allah yana ko’ina to yana nufin komai Allah ne kenen, saboda haka kafircinsa ya fi na mushrikai, haka nan kafircinsa ya fi na kiristoci masu cewa Allah uku ne.
Amma idan muka lura za muga cewa dan aka ce Allah yana sama to babu makawa sai ya kasance ya keɓanta da wani waje, idan kuwa ya keɓanta da wani waje to dole ne ya kasance yana da iyaka, idan kuwa ya kasance yana da iyaka, to dole ne ya kasance yana da farko, kuma yana da ƙarshe, idan kuwa Allah ya kasance yana da farko, kuma yana da ƙarshe, dole ne ya zamanto akwai wani lokaci da babu Allah, kuma a nan gaba ma Allah zai kasance ya ƙare  babu shi, wannan kuwa shi ainahin kore samuwar Allah.
Amma duk da haka Ibn Taimiyya da mabiyansa sun nanace a kan cewa Allah yana zaune a kan al’arshi, kuma, yana keɓance a sama idan yana da buƙatar zuwa ƙasa sai ya sauko ya biya buƙatun bayi sannan ya koma mazauninsa a can sama

AttachmentSize
File fae88ad50b488e7733e237cc0b26ffd7.mp421.56 MB