Ibn Taimiyya da tauhidi Ma’anar al’arshi riwayoyin Ahlul Baiti-1

Riwayiin da aka rawaito da ƴ’aƴ’ ɗakin Annabi Muhammad ( saww) sun bayyan cewa: a cikin alƙur’ani an ambaci kalmar al’arshi a wurare daban – daban, duk inda aka ambace shi kuwa ya na ma’ana daban da ta wani wajan, misali wani lokacin idan aka ambaci al’arshi to yana nufin mulkin Allah, kamar inda Allah yake cewa( Allah Arrahmanu ya daidaita a kan al’arshi) wato ya daidaita a kan mulkin, ma’ana dai shi ne mai mulki babu wani abu wanda ya fita daga cikin mulkin Allah.
Amma gaba ɗaya al’rshin ɗaya abin da Allah ya ke nufi a cikin Alƙur’ani shi ne ilimin gaibu ne na Allah (saww), wato al’arshi da kursiyyu suna nufin ilimin Allah na gaibu, Allah shi ne masanin duk abin da ya halitta kafin halittarsa, da lokacin da yake halittarsa, da kuma bayan ya halicceshi, saboda haka shi ne ya san ya ya zai gudanar da al’amuran wannan halittar, sannan shi ne dai yake gudanar da komai, shi ne Allah ya ce:
( رب العرش العظيم)
wato daial’arshi da kursiyyu suna nufin ilimin Allah na gaibu, shi kuma wannan gaibun yana da kofa ta zahiri itace kursiyyu, shi kuma al’arshi shi ne kofar ilimin ta baɗini.

AttachmentSize
File f463da92f8a2ffa1943a35ebd40bb15e.mp435.6 MB

Ƙara sabon ra'ayi