TARIHIN IMAM HUSAIN (AS) ( 14)

 Cigaban hadisin da yake magana akan wasiyyoyin Annabi (saww)Ya Muhammad! Da a ce wani bawa daga cikin bayina zai bauta min har sai ya zama yanke ( wato har sai ya mutu saboda bauta) kokuma sai ya rame, sannan ya zomin yana mai jayya da wilayarku, da ba zan gafarta masa ba, har sai ya yi iƙrari, kuma ya yarda da wilayarku. Ya Muhammad shin kana so ka gansu?.Sai na ce: na’am ya Ubangijina.Sai ya ce: dani ka waiwaya ka kalli daman al’arshi, Sai na waiwaya, sai gani da Aliyyu, da Faɗima, da Hasan da Husaini, da Aliyyu ɗan Husain, da Muhammad ɗan Aliyyu, da Ja’afar ɗan Muhammad, da Musa ɗan Ja’afar, da Aliyyu, ɗan Musa, da Muhammad ɗan Aliyyu, da Alyyu ɗan Muhammad, da Hasan, Aliyyu, da Mahdi, suna cikin walwalin wani haske suna tsaye suna salla, shi kuma Mahadi yana tsakiyarsu, kamar wani tauraro mai walwali. Sai Allah ya ce ya Muhammd! Waɗannan sune hujjojina, shi kuma wannan na tsakiyar tasu shi ne mai daukar fansa a cikin  tsatsonka, na rantse da ɗaukakata da buwayata, Mahadi shi ne hujja wajiba ga waliyyaina, kuma shi ne mai ɗaukar fansa akan maƙiyana.

AttachmentSize
File 85779910ce38f7f63c361457d5375fd5.mp421.72 MB

Ƙara sabon ra'ayi