TARIHIN IMAM HUSAIN( AS) 21

Bayan sojojin Yazidu sun kashe imam Husain (as) sun yi ta kokarin su kshe imam Aliyyu Zainul abidina babban dan imam husain, saboda a wannan lokacin ya kasance yana tsananin rashin lafiya, hakan ta sa ya rame harma wasu suna ganin cewa yaro ne karami wanda ma kobalaga ma bai yi ba, ammam duk da haka sun yi kokarin su kashe shi, domin sun dau alwashin karar da zuriyar Annabi Muhammad (saww), sayyida Zainab kanwar imam husain ita ce ta tsaya kai da fata tana makalkaleshi ta cewa: wallahi ba za'a kashe bas ai dai a kashe ni tare dashi, haka dai Allah yak are ba su iya kashe ba domin Allah ya yi alkwarin wanzar da zuriyar gidan Annabi (sawa) don haka ne duk yunkurin da suka yi na kashe shi ya ci tura.
Bayan an gama karkashe, imam Husain da sahabbansa sai aka sassare kawukansu wato aka raba kuwakansu daga gangar jikunansu.
Sannan aka aika dasu izuwa ga Ubaidullahi ibn Ziyad gwamnan Yazidu na birnin Kufa.
Bayan haka sai a ka yi ta kewayawa da wadannan kuwukan da kuma ribatattun iyalan gidan Annabi(saww).
 
Sannan daga baya ibn Ziyad ya aika dasu zuwa Dimask can kasar Sham bisa Umarnin da Yazidu yayi 

AttachmentSize
File 96e35b21701b2638a0c6210d520e9a36.mp415.13 MB