TARIHIN IMAM HUSAIN( AS) (20)

A cikin wunin rana ta goma ne aka  kashe shugaban shahidai shugabanmu imam Husain da da ƴ’aƴ’ansa, da ƴ’aƴ’an ɗanuwasa imam Hasan, (as) da ƴ’an’uwansa da sahabbansa (as).
An rawaito daga imam Baƙir cewa: an sassari imam Husaini ɗan Ali (as) har sai da aka sami sara a jikinsa guda ɗari uku 300,m  da suka guda ashirin da ƴ’ankai, wanda aka yi masa kodai suka da mashi, ko sara da takobi, kokuma harbi da kibiya.
 
 Don haka wannan rana rana ce da baƙin cikin iyalan gidan Annabi, (saww) da shi’arsu yake ƙara zama sabo, don haka ya kamata ga shi’arsu, da masoyansu su bar duk wasu ayyuka na rashin dacewa musamman a cikin wannan rana, sannan su ringa shirya majalisoshi na ta’aiyya, da barin cin abinci ko shan wawani abin sha  har zuwa lokacin zawalin rana, sanna su tafi ziyarar Kabarin imam Husain, haƙiƙa an rawaito cewa: duk wanda ya ziyarci imam Husain ranar Ashura to kamar kamar ya ziyarci Allah ne a Al’arshinsa.

AttachmentSize
File 027ca55db48c87468a8f1cb821ce9a8c.mp417.02 MB

Ƙara sabon ra'ayi