ANNABTA (19)

Dukkanin Musulmin duniya tun daga lokacin sahabbai har izuwa wannan zamani da muke ciki suna girmama fiyayyenn halitta Annabi muhammad (saww) kuma suna neman tabarukinsa, suna yin tawassuli da shi, wannan ita ce koyarwarAlƙur’ani da sunnar Annabi (saww), sannan kuma sun yi imani da cewa Annabi ya fito daga tsatso mai tsarki; wato iyayensa tun daga kan Annabi Adamu da Hauwa har izuwa kan Abdullahi da Amina tsarkaka ne, ba a taɓa samun kafiri, ko mazinaci, kokuma mai wata mummunar aƙida, ko mummunar ɗabi’a ba a cikin jerin kanninsa.
Amma banda wahabiyawa, domin su suna hana kowa ya sami albarkar Annabi (saww), suna hana tawassuli da shi, suna hana neman albarkarsa, don ƙiyayya a gareshi da kuma, saɓawa koyarwa Alƙur’ani da sunnar fiyayyen halitta. Annabi muhammadu (saww).
Sannan abin takaici suna kafirta iyayensa wato sayyuidina Abduullahi da sayyidatuna Amina Allah ya ƙara musu yarda.    

AttachmentSize
File e213a5a6e144d3da4ddf5d80f219e35c.mp420.63 MB