TAUHIDIN IBN TAMIYYA YA YA SAƁA DA TAUHIDIN AHLUL BAITI (3)

Ibn Taimiyya yan cewa: babu wata aya ta Alƙur’ani ko wani hadisi, kokuma magana daga salaf (magabata) da ta ce siffofin Allah ba gaɓɓai bane, duk da cewa akwai maganganun imam Aliyyu (as) waɗanda ya ke cewa: Allah ba shi da gaɓɓai, amma Ibn Taimiyya ya rufe idanuwansa, ya ce babu wani salaf da ya faɗi haka, koda yake babu mamaki tun da shi Ibn Taimiyya yana gaba da ƙiyayya da imam Aliyyu (as), don haka ne ma bai ɗauke shi a matsayin wani abin koyi ba, ballantana ya dauki maganarsa, a matsayin hujja.
Malaman Ahlussunna, sun tabbatar da cewa duk ayoyinj da suke magana a kan siffofi misalin hannu da fuska da makamantansu ayoyine mutashabihai, wato ayoyi ne da suke da buƙatar a fassara da ma’anar abin da ya da ce tsarkin da ɗaukaka ta zatin Allah, ba a kan zahirin abin da suke  kai ba.
Maganar ayoyi muhkamai da mutashabihai kuwa Allah shi ne ya tabbatar mana da cewa a cikin alƙur’ani a kwai ayoyi muhkamai da kuma ayoyi mutashabihai. 

AttachmentSize
File fd9b7b6758ddfb07196dfc98c08169c0.mp415.81 MB

Ƙara sabon ra'ayi