TAUHIDIN IBN TAMIYYA YA YA SAƁA DA TAUHIDIN AHLUL BAITI (2)

Ibn Tamiyya ya nanace a kan cewa idan aya ta Alƙu’rani ko kuma wata riwaya, ta ti magana a kan hannu, ko ƙafa a cikin abubuwan da suka shafi zatin Allah to dole ne a tafiyar da wadannan kalmomin a zahirin lafazinsu, misali Allah yana cewa:
(وقالت اليهود يد الله مغلولة غلت أيديهم ولعنوا بما قالوا)
(Yahudawa sun ce hannun Allah a ɗaure yake, an ɗaure hannuwansu, kuma an tsine musu saboda abin da suka faɗa)
Sannan Ibn Taimiyya yana cewa idan ga ainahin ma’anar kalma aharshen larabci to ba za a fassar ta majaz ba, sai dai idan da ƙarina a kan haka.
Malamai suna cewa Haƙiƙa haƙiƙa wannan aya da makamantanta ba sa nuna cewa hannun da aya take magana a kansa yana nufin cewa Allah yana da hannu wanda yake da ma’anar gaba kamar yadda aka sani, domin faɗar hakan jingina naƙasu ne ga Allah, shi kuwa dangana naƙasu ga Allah, rusa imani ne. Don haka ne ƙofar ilimin Annabi (saww) wato imam Aliyyu ɗan Abu Ɗalib (as) ya faɗa a gurare da dama cewa ba’a jingina gabbai ga Allah( T) domin yin haka kafirci ne.

AttachmentSize
File 8d111869ed1a635712579e7e423f159a.mp420.46 MB