An yi gargadin komawar 'yan ta'addar kasar Belgium 200 da suke cikin IS zuwa Turai

An yi gargadin komawar 'yan ta'addar kasar Belgium 200 da suke cikin IS zuwa Turai

Magabatan kasar Belgium sun ce kimanin 'yan kasar 200 ne dake cikin kungiyar 'yan ta'addar ISIS suke kokarin komawa Turai domin kaddamar da hare-haren ta'addanci.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Jan Jambon ministan cikin gidan kasar Belgium a yau juma'a na cewa magabatan leken asirin kasar sun sanar da su cewa kimanin 'yan kasar 200 ne da suka yaki kalkashin kungiyar ISiS a kasar Siriya suke kokarin komowa kasashen turai domin kaddamar da kai hare- haren ta'addanci, domin haka wajibi ne magabatan na Turai su sanya ido sosai domin tunkarar wadannan 'yan ta'adda, kuma wannan lamari na zuwa ne bayan matsin lamabar da kungiyar ta ISiS ke fuskanta a kasar ta Siriya.
Kafin wannan sanarwar da Ministan kasar Belgium, manya-manyan kungiyoyin tsaron na kasashen Turai sun sanar da cewa kimanin 'yan kasashen 5000 da suka samu horo daga kungiyar Da'esh (ISIS) suka koma kasashen na Turai, da hakan ya sanya yankin ke fuskantar barazanar ta'addanci, domin haka wajibi ne magabatan tsaro su sanya ido sosai kan mutanan.
Ministan cikin gidan na Belgium ya tabbatar da cewa barazanar komawar 'yan ta'addar zuwa gidajensu abin damuwa ne na har abada ga gwamnatocin kasashen Turai.

Ƙara sabon ra'ayi