Yawan Mutanen Da Suka Rasa Rayukansu A Girgizar Kasar Equador Sun Haura 600

Hukumar Kula da Hatsarurruka a kasar Equador ta sanar da cewa; Yawan mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon girgizar kasa a yankin arewa maso yammacin kasar sun haura mutane 600 tare da jikkatan wasu dubunnai.
Kamfanin dillancin labaran kasar China Shin Huwa ya watsa rahoton cewa: Yawan mutanen da suka rasa rayukansu tun bayan faruwar girgizar kasa a yankin arewa maso yammacin kasar Equador a ranar Alhamis da ta gabata sun haura zuwa 602, yayin da yawan wadanda suka jikkata suka haura zuwa 12, 000 da dari 492, sannan wasu kimanin 130 suka bace har yanzu babu labarinsu.
Har ila yau girgizar kasar ta janyo rushewar gidaje 998,000 tare da lalata wasu 740,000 na daban. A halin yanzu haka dai Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar da shawarar tallafa wa jama'ar da masifar girgizar kasar ta ritsa da su da kudade dalar Amurka miliyan 72.7 domin samun farfadowa.

Ƙara sabon ra'ayi