Palasdinawa Uku Sun Yi Shahada Sakamakon rubtawar Hanyar Karkashin Kasa A Kansu

Rubtawar hanyar karkashin kasa da Palasdinawa suke yi a tsakanin kan iyakar yankin Palasdinu da kasar Masar ta yi sanadiyyar shahadar Palasdinawa uku.

 

 

Kafar watsa labaran Qudus mallakin Palasdinawa ta bada labarin cewa; Wasu Palasdinawa uku sun yi shahada sakamakon runtawar hanyar karkashin kasa da suke amfani da ita domin samun damar jigilar kayayyakin bukatun yau da kullum tsakanin yankin Palasdinawa da kasar Masar.

 

Rubtawar hanyar karkashin kasar ta auku ne a yankin kudancin garin Rafah da ke Zirin Gaza kusa da kan iyaka da kasar Masar, kuma Palasdinawan suna samun damar shigar da kayayyakin bukatun yau da kullum ne daga kasar Masar zuwa ga al'ummunsu ta hanyar karkashin kasar sakamakon killace yankin Palasdinu da aka yi yau tsawon shekaru kimanin goma lamarin da ya wurga al'ummar ta Palasdinu cikin mawuyacin halin rayuwa.