Kungiyar Ansarull..ta yi alawadai da karya yarjejjeniyar tsagaita wuta daga saudiya

Kakakin kungiyar Ansarull...ya yi alawadai ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri cikin kasar sa daga sojojin hayar kasar Saudiya.

Muhamad Abdussalam kakakin kungiyar Ansarull....ya ce duk da irin yarjejjeniyar tsagaita wutar da aka cimma a kasar to amma masarautar Ali-sa'oud na ci gaba a kai hare-haren wuce goma da iri a wasu yankunan kasar, kuma hakan na iya jefa yarjejjeniyar tsagaita wutar cikin hadari tare kuma da ragewa tattaunawar sulhun da za a yi a kasar Kuwait armashi.

Gidan telbijin din Almasira na kasar Yemen ta Gwado jiragen yakin masarautar Ali-sa'oudsuna kai hari tare da karya yarjejjeniyar tsagaita wuta a jihohin kan iyakar kasar wato jahohin Hijja da Sa'ada a jiya Litinin.

Har ia yau a jiya Lititin din jiragen yakin masarautar Ali sa'oud sun yi ruwan bama-bamai a yankin Almutun dake jihar Ta'az.

Daga lokacin da yarjejjeniyar tsagaita wutan ta fara aiki an karya yarjejjeniyar sama da 40 a sassa daban daban na cikin kasar kamar yadda majiyar labaran kasar ta ijyo.

Kafin hakan mai magana da yawun gamayar sojojin hayar dake kai hare-haren wuce gona da irin kan Al'ummar kasar Yemen na Saudiya ya bayana cewa za su mutunta wannan yarjejjeniya wacce ta fara aiki tun a jijjifin safiyar jiya Litinin.

Ƙara sabon ra'ayi