Adadin Mutanan da suka mutu sanadiyar Gobara a kasar Indiya ya haura dari

Sakamakon tashin gobara a wurin ibada na mabiyar Addinin Hindu a kasar Indiya sama da Mutane 100 suka hallaka yayin da wasu 250 suka jikatta

 

Wannan gobara ta tashi ne a wurin ibadar Putugal divai na garin Kulan a jihar Kerala dake kudancin kasar a yayin da mabiya addinin Hindu suka taru domin bukin zagayowar sabuwar shekarar su.

Rahoton ya ce gobarar ta yi sanadiyar lalacewar ginin baki dayansa kuma daga cikin wadanda suka hallakar har da jami'an 'yan sanda.

Jami'an tsaro da sauran masu ayyukan agaji na ta aikin ceto a inda aka sami wannan hasarar rayuka. baya ga hakan an kai Ayarin likitoci da magunguna zuwa wurin.

Ita dai wannan gobara ta tashi ne da misalin karfe 3:00 na Asufahin yau, yayin da mahalarta wurin suka shagaltu da bukukuwansu.

Jami'an 'yan sanda sun sanar da cewa mai yi yuwa gobarar ta tashi sanadiyar bashewar runbun tsimin da aka tanada na kayan wasan wuta dake cikin wurin ibadar.

Yanzu haka dai likitoci da masu agaji sun shagaltu da yiwa wadanda suka jikkata magani bayan da aka samun nasarar kashe gobarar.

Ƙara sabon ra'ayi