Gwamnatin Belgium Ta Sanar Da Ci Gaba Da Tsaurara Matakan Tsaro A Kasar

Gwamnatin Belgium Ta Sanar Da Ci Gaba Da Tsaurara Matakan Tsaro A Kasar

Firayi ministan kasar Belgium ya sanar da cewa gwamnatin kasar za ta ci gaba da tsaurara matakan tsaro da zama cikin halin ko ta kwana duk kuwa da kame wani adadi na wadanda ake zargi da hannu cikin harin ta'addancin da aka kai wa kasar kwanakin baya

 

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya jiyo firayi ministan kasar ta Belgium Charles Michel yana sanar da hakan inda ya ce duk da nasarar da jami'an tsaron kasar suka samu na kama wasu daga cikin wadanda ake zargi da hannu cikin harin ranar 22 ga watan Maris din, to amma duk da haka dai za a ci gaba da zama cikin halin ko ta kwana a kasar don fada da barazanar ta'addanci da kasar ta ke fuskanta.

A jiya ne dai babban mai shigar da kara a kasar Belgium din ya sanar da cewa jami'an tsaron kasar sun sami nasarar kame wasu mutane hudu da ake zargi da hannu cikin wannan aiki na ta'addanci ciki kuwa har da Mohamed Abrini wanda aka fi sani da Mai Malafa, wanda jami'an tsaron kasar suke nema ruwa a jallo saboda zargin yana da hannu cikin harin da aka kai kasar da kuma wanda aka kai kasar Faransa a shekarar da ta gabata.

A ranar 22 ga watan Maris din da ya gabata ne 'yan ta'addan suka kai hari filin jirgin sama da kuma tashar jiragen kasa na birnin Brussels din lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 35 da kuma raunata wasu da dama.

.

Ƙara sabon ra'ayi