Sudan ta yi alkawarin aiki tare da tarayyar Turai a yaki da Ta'addanci

Gwamnatin Sudan ta yi alkawarin aiki tare da kungiyar tarayyar Turai a yaki da Ta'addanci da kuma batun 'yan gudun hijra

 

 

Kafar watsa labaran Qudus Al-arabie ta nakalto Abdulgani Anna'im mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sudan a yayin ganawarsa da wakilin kungiyar tarayyar Turai ya bayyana shirin kasar sa na aiki tare da kungiyar EU kan batun 'yan gudun hijra, samar da konciyar hankali a kasashen dake makwabtaka da kasar, da kuma yaki da ta'addanci, har ila yau Anna'im ya shawarci EU da kafa wani kwamitin kasa da kasa wanda zai bayar da shawarwari kan abin da ya shafi yankin.

Har ila yau Anna'im ya bayyana kyakkyawan fatantansa gakungiyar ta EU na taimakawa kasar domin kawo karshen rikicin yankin Darfur da kuma takunkumin da aka kakaba mata na tattalin arzikin kasar

A nasa bangare, wakilin kungiyar tarayar turai ya bayyana cewa manufar ziyarar ta sa a kasar Sudan, tattaunawa da magabatan kasar kan kan matsalar karamcin abincin da kasar ke fama da shi, gudanar da bincike kan matsalar 'yan gudun hijra,tare kuma da samar da abinci gami da samar da tsaro a iyakokin kasar.

Ƙara sabon ra'ayi