Al-Qa'ida Ta Tabbatar Da Hallaka Daya Daga Cikin Manyan Shugabanninta A Siriya

A karon farko kungiyar Al-Qa'ida ta tabbatar da halakar daya daga cikin manyan shugabannin reshen kungiyar a kasar Siriya bayan wani hari da sojojin Siriya suka kai masa ta sama inda suka sami nasarar hallaka shi tare da wasu na kurkusa da shi.

 

 

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar kungiyar Al-Qa'idan reshen arewacin Afirka (AQIM), cikin wata sanarwa da ta fitar, ta tabbatar da hallaka Abu Firas al-Suri, daya daga cikin shugabannin kungiyar ta'addancin nan ta Jabhatun Nusra a kasar Siriya biyo bayan wani hari da jiragen yakin Siriya suka kai masa a a ranar Lahadin da ta gabata.

Shi dai Abu Firas al-Suri wanda kuma har ila yau ake kira da Radwan Nammous, daya ne daga cikin manyan shugabannin kungiyar ta'addancin nan ta Jabhatun Nusra, wacce take a matsayin wani bangare na kungiyar Al-Qa'ida a kasar Siriya, kana kuma ya kasance daga cikin membobin majalisar shura ta kungiyar da ake zargi da jagorantar wani adadi mai yawa na 'yan ta'addan da suke yaki a kasar Siriya.

A ranar Lahadin da ta gabata ce sojojin Siriya suka kai masa hari ta sama a wani kauye da ke arewa maso yammacin garin Idlib na kasar Siriya inda suka hallaka shi tare da wasu 'yan ta'addan da aka ce sun kai ashirin ciki kuwa har da dansa da kuma wasu 'yan ta'adda 'yan kasar Uzbekistan.

Ƙara sabon ra'ayi