Kasar Salio Tana Shelanta Rabuwa Da Annobar Cutar Ebola Na Baya Bayan nan.

 Majalisar dinkin duniya ta bada sanarwan cewa kasar Salio ta rabu da annoban
Majalisar dinkin duniya ta bada sanarwan cewa kasar Salio ta rabu da annoban cutar Ebola bayan an kwace kwanaki 42 babu wanda ya kamu da ita. Kamfanin dillancin labaran AFP ya nakalto majiyar Hukumar lafiya ta duniya WHO tana bada sanarwan haka a yau Alhamis.
Hukumar ta kara da cewa tana taya mutanen salio murnar rabuwa da wannan annoban, bayan kwanaki 42, wato tswo rayuwar kwayoyin cutar na Ebola har sau biyu kenen.
A wani jawabin da ya gabatar da gidan television na kasar Ministan kiwon lafiya na kasar Salio Dr Abubakar Fofanah ya yabawa dukkan mutanen salio don hadin kai da suka bawa gwamnati da jami'an kungiyoyin kasa da kasashe don yakar wannan annoban.
Cutar Ebola dai ta kama mutane dubu 28600 a cikin kasashen ukku wadanda abin ya fi shafa a yammacin Afrika, kuma rabin wadanda ta kaman a kasar Salio suke. Mutane dubu 11,300 ne cutar ta kashe tun lokacinda ta bulla a karshen shekara ta 2013.

Ƙara sabon ra'ayi