MDD: Yakin Sudan Ta Kudu Ya Lakume Rayukan Akalla Mutane 50,000

Yaki na tsawon shekaru biyu a kasar Sudan ta Kudu ya cinye rayukan mutane akalla 50,000

 

 

Yaki na tsawon shekaru biyu a kasar Sudan ta Kudu ya cinye rayukan mutane akalla 50,000. Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto wani jami'im majalisar dinkin duniya yana fadar haka a jiya Laraba. Ya kuma kara da cewa duk tare da yerjejeniyar da bangaren shugaban kasa na yan tawaye suka cimma a watan da ya gabata har yanzun muna ganin rikici kabilanci yana ci gaba a wasu yankunan kasar.

Jami'in ya kara da cewa banda wadanda aka kashe yakin basasar kasar sudan ta kudu ya tilastwa mutane akalla miliyon 2.2 barin gidajensu.

A shekara ta 2013 ne mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu Reack Marcher ya fara tawaye bayan da aka sauke shi kan kujerarsa. Kuma bayan yaki na shekaru biyu bangarorin biyu sun cimma yerjejeniya ta zaman lafiya, inda shugaban kasar Silver Kiir ya maida Marcher kan kujerar shugabancin kasar . sai dai a bangaren tsagaita bude wuta ko wani bangare yana zargin dayan wajen rashin mutunta yerjejeniyar sulhun.

Majalisar majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa akwai barazanan mutuwar mutane a kasar sanadiyyar karancin abinci nan da yan watanni masu zuwa. Don haka jami'an ya bukaci shuwagabannin kasar su gaggauta samar da zaman lafiya don a sami damar kaiwa mutanen dauke kafin lokaci ya kure.

Sudan ta kudu dai ta sami 'yanci daga kasar Sudan a shekara ta 2011 kuma ba'a yi shekara guda ba rikicin da kasar take ciki a yanzu ya kunno kai.

Ƙara sabon ra'ayi