MDD Da Kungiyoyin Agaji Zasu Agazawa Siriyawa 154,000

MDD da kungiyoyin agaji na kasa da kasa sun ce a shirye suke domin agazawa wasu 'yan kasar 154,000 dake cikin mawuyacin hali a wasu yankunan kasar dake da wahala shiga.

 

 

Wannan dai na zuwa a kwanaki na uku bayan yarjejeniyar tsagaita musayar wuta da majalisar dinkin duniya ta dauki nauyi ta fara aiki.

 

Bangarorin da suka hada da MDD da kungiyoyin agaji sun nuna damuwa matuka game da halin da dubban Siriyawa ke ciki, wanda suka ce a shirye suke taimaka masu a cikin kwanaki biyar masu zuwa kamar yadda babban jagoran harkokin jin kai a kasar ta Siriya Yacoub El Hillo ya sanar a jiyya lahadi.

 

Kazalika babban jami'in ya kara da cewa da zarar sun samu amuncewa masu rikici a kasar, to a shirye suke su agazawa mutanen kasar dake cikin mawuyacin hali da yawan su ya kai miliyan 1,7 wadanda galibin su ke cikin wurare masu wahala shiga.

 

MDD tayi kiyatsin cewa kimanin Siriyawa 500,000 ne ke cikin wurare mafi wahala shiga, yayin da wasu milyan 4,6 ke rayuwa a wuraren dake da wahala isar da kayan agaji.

Ƙara sabon ra'ayi