Fada Da Bokoharam A Kasar Kamaru

Musulmi Da Kiristoci Sun Hada Kai Domin Fada Da Bokoharam

 


 

 

Musulmi da mabiya addinin Kirista a kasar Kamaru sun fito da wani shiri na hadin guiwa domin fada da kungiyar bokoharam.

 

Kafar watsa labaru ta Afirca Time, ta buga a shafinta na interntet cewa, sabon shirin ya kunshi bada kariya da mabiya addinan za su rika yi wa wuraren ibadarsu.

A cikin garuruwa shida na arewacin kasar ta Kamaru, musulmi da mabiya addinin kirista sun rika kare wuraren ibadarsu domin hana kungiyar bokoharam kai musu hari.

Gwamnan yankin Mijinyawa Bakar ya shaidawa manema labaru cewa; Shirin ya haifar da Da, mai ido a wuraren da aka zartar da shi, kuma suna son ganin ya watsu a wusu wurare.

Ƙara sabon ra'ayi