Sojojin Siriya Sun Kwato Wasu Garuruwan 'Yan Shi'a Biyu Daga Hannun 'Yan Ta'adda

Sojojin Siriya Sun Kwato Wasu Garuruwan 'Yan Shi'a Biyu Daga Hannun 'Yan Ta'adda

Sojojin kasar Siriya da kawayenta na dakarun kungiyar kungiyar Hizbullah sun sami nasarar kawo karshen kawanya na shekaru uku da 'yan ta'adda suka yi wa wasu garuruwa biyu na mabiya tafarkin Shi'a lamarin da ya katse daya daga cikin hanyoyin da 'yan ta'addan suke samun makamai daga kasar Turkiyya.

Gidan talabijin din kasar Siriyan ya bayyana cewar dakarun kasar Siriyan sun sami nasarar fatattakan 'yan ta'addan da suka kawanya wa garuruwan Nubul da Zahraa da suke da mutanen da suka kai kimanin dubu 60,000, bayan gumurzu na kimanin kwanaki uku a ci gaba da kwato yankunan da suke lardin Halab da ke arewacin kasar Siriyan.

Kwato wadannan garuruwan dai ya ba wa sojojin Siriyan nasarar kwato mafi yawa daga cikin yankunan da 'yan ta'addan suke rike da su, wanda hakan wata nasara ce da za ta iya katse dukkanin hanyoyin da 'yan ta'addan suke samu wajen isar da makamai da kayayyakin da suke bukata zuwar garin na Halab.
Sojojin Siriyan da kawayensu na kungiyar Hizbullah suna ci gaba da matsin lamba a kan 'yan ta'addan da nufin korarsu daga garin na Halab mai matukar muhimmanci ga dukkanin bangarori biyun.

Ƙara sabon ra'ayi