Abubakar Bagdadi jagoran 'yan ta'addan Daesh ya tsere zuwa Libya

Shafin yada labarai na Sporting ya bayar da rahoton cewa, jagoran kungiyar yan ta'adda ta Daesh Abubakar Bagdadi ya tsere zuwa kasar Libya.

 Rahoton ya ce Abubakar bagdadi ya samu raunuka a wani hari da jiragen yakin kasar Iraki suka kai kan ayarin motocinsa a kwanakin baya, kuma tun daga lokacin yana kasar Turkiya ana kula da lafiyarsa awani asbitin sojin gwamnatin Turkiya, amma daga bisani ya koma birnin Sirte na kasar Libya.

A nasa bangaren kakakin ma'aikatar harkokin cikin gida a hukumar Tubruk da aka amince da ita a majalisar dinkin duniya Tarik Kharraz ya bayyana cewa, sakamakon hare-haren da jiragen yakin kasar Rasha suke kaiwa garin Riqqah na Syria babbar tungar 'yan ta'addan Daesh, hakan ya sanya kungiyar mayar da birnin Sirte na kasar Libya da ke karkashin ikonsu a halin yanzu a matsayin sabuwar tungarsu.

Ƙara sabon ra'ayi