Takurawa Mata Musulmi a cikin Nahiyar Turai

Takurawa Mata Musulmi a cikin Nahiyar Turai

Takurawa Mata Musulmi a cikin Nahiyar Turai

AllahءMusulunciءAddiniءMohammadءAliءshiءmahdiءtvshiaءTakurawa Mata Musulmi a cikin Nahiyar Turai

Daruruwan 'yan mata musulmi sun yi zanga-zanga a kasar Beilgium suna masu bayyana kin amincewarsu akan takurawar da ake yi musu. Gwamnatin kasar ta Beilgium dai ta bayyana sanya suturar hijabi da mata musulmi su ke yi a matsayin wanda ya ci karo da tsarin da kasar ta ke bi na raba addini da siyasa. Saboda haka gwamnatin kasar ta fito da wasu sabbin dokoki da za su hana 'yan mata musulmi daura suturar hijabi a cikin makarantun kasar.Wannan ya maida Beilgium zama kasa ta biyu da ta hana dalibai mata musulmi daura hijabi a cikin makarantu.Gwamnatocin Turai suna bugun kirji da kuma yin takama da bada 'yanci ga al'umma amma ga shi suna yi wa mata musulmi dabaibayi akan hakkinsu na zabar suturar da za su daura. Addinin musulunci yana ganin mace da kima wanda sanya suturar hijabi yana cikin wannan girmamawar da ya ke mata. Abu ne da babu shakku a cikinsa cewa Allah ya halicci mace da siga mai kyau da sanyin hali saboda ta zama mai taka rawa a matayinta na uwargida sannan mahaifiya.Abin takaici ne cewa yadda ake daukar mace a yammacin Turai bai wuce wata haja ba, ana kuma amfani da kyawun da Allah ya yi mata domin yin tallace-tallacen kayan masa rufi. Ita mace daidai ta ke da namiji ta fuskar 'yanadamtaka da hakkin bil'adama saboda haka bai kamata ace ana amfani da kyawun halittarta ba a matsayin abin talla da zummar cin riba. Sanya tufafin hijabi yana a matsayin bada kariya ne ga ita mace daga masu mugun nufi.Babu wani aiki da mace ba za ta iya yi ba saboda tana sanye da suturar hijabi ko kuma taka rawar da ta dace da ita a cikin al'umma. Fiye da haka ma sanya hijabin da mata suke yi zai samar da tsaro da kariya a cikin al'umma a lokacin da su ke gudanar da ayukansu ba tare da wata matsala ta azo a gani ba.Duk da rawar da hijabi ya ke takawa wajen baiwa mace kariya da kare mutumcin iyali, amma adawar da yammacin turai su ke nunawa musulunci ya sa idanunsu sun rufe akan hakan.Hana dalibai mata musulmi daura suturar hijabi take hakkin biladama ne da kuma 'yanci na daidaiku wanda su kansu kasashen turai su ke bugun kirji da karewa.Kin jinin musulunci a nahiyar turai yana da dogon tarihi, sai dai ya kara yaduwa ne a nahiyar turai bayan cin nasarar juyin musulunci a Iran a 1979.Nasarar da juyin musuluci ya samu ya bude wata sabuwar kofa ne ga al'ummun da ake zalunta a duniya. Ya kuma sa masu yanci a tunani hatta a cikin nahiyar ta turai sun fara gudanar da nazari da bincike akan addinin musulunci. Haka nan kuma ya sa mutane sun koma ga addini da riko da shi a cikin harkokinsu na rayuwa. Bunkasar da musulunci ya ke samu a cikin kasashen turai din ya sa akidun da su ke raba addini daga siyasa su ka shiga tsaka mai wuya. Da akwai masana da dama na turai wadanda su ka musulunta saboda ganin gaskiya a cikinsa da kuma kiransa zuwa ga shimfida adalci.Gwamnatocin turai wadanda su ka ja daga wajen fada da yaduwar musulunci a cikin al'ummunsu sun rika daukar tsauraran matakai da hana musulmi sakat. Haka nan kuma sun bude kafafen watsa labarunsu domin bada dama ga duk wanda ke son bakanta sunan musulunci da cin zarafinsa.Gwamnatocin yammacin turai ne su ka bada kariya ga Salman Rushdi wanda ya rubuta littafin :"Ayoyin Shaidan." a 1980 da a cikin ya ci zarafin abubuwa masu tsarki na musulunci.Gwamnatoci da dama na turai ba su tsaya anan ba sun ma rika sukar musulmi saboda sun nuna rashin amincewarsu akan waccan littafi na Salman Rushdi.Sannu a hankali kasashen turai sun rika daukar matakai na takurawa musulmi a cikin kasashensu. Daga cin zarfin musulunci zuwa hana mata sanya hijabi a cikin makarantu. Faransa ce kasa ta farko wacce ta yi doka akan hana sanya jihabi a cikin makarantu. Ga shi kuwa wannan kasa tana daukar kanta cibiyar yanci da demokradiyya. Hana sanya hijabi da sunan cewa yana cin karo da tsarin sakulanci na raba addini da rayuwa, ya watsu daga faransa zuwa wasu kasashe. A cikin wasu kasashen turai na hana mata rufe fuskokinsu a wuraren da jama'a ke taruwa.Wadannan irin matakan da kasashen na turai su ke dauka ya jawo maida martani daga kungiyoyin kare hakkin dan'adam. Kotun Koli ta kasar Faransa wacce ta karbi koke-koke ta fitar da bayanin da ke nuni da cewa yin doka domin hana sa hijabi za iya cin karo da tsarin mulkin kasar. Tomas Hammerbourg wanda ya ke cikin kwamitin koli na kwamitin kare hakkin dan'adam a turai ya ce: "Hana mata su rufe fuskokinsu tsoma baki ne wanda bai dace ba akan rayuwar daidaikun mutane."Wannan jami'in na kare hakkin bil'adam ya kuma kara da cewa: "Daukar wannan matakin zai iya cin karo da dokokin nahiyar turai."

Ƙara sabon ra'ayi