Ma'aikatar Harkokin Wajen Siriya Ta Ja Kunnen John Kerry

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Siriya ta bayyana maganganun baya-bayan nan da sakataren wajen kasar Amurka John Kerry ya yi kan kasar ta Siriya a matsayin tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar da ba za a taba amincewa da shi ba.

 

 Kamfanin dillancin labaran kasar Siriyan SANA, ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar, cikin wata sanarwa da ta fitar, tana cewa maganganun John Kerry kare tsaye ne ga hakkin da al’ummar Siriya suke da shi na zaban abin da suke son wanda kuma yake barazana ga yiyuwar samun nasarar taron sulhu na Geneva 2 da za a gudanar.

 

Ma’aikatar harkokin wajen na Siriya ta kara da cewa ya kamata John Kerry ya san cewa al’ummar Siriya ne kawai suke da hakkin zaban shugabansu da kuma siyasar kasarsu ba tare da tsoma bakin wata kasa ta waje ba.

 

Ma’aikatar harkokin wajen na Siriya tana mayar da martani ne ga kalaman sakataren harkokin wajen na Amurka a wata ganawa da manema labarai da ya yi da takwaransa na kasar Masar a birnin Alkahira inda ya ce ci gaba da shugabancin Bashar al-Asad a Siriya matsala ce ga kasar.